in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum goma a jihar Anambara
2018-09-26 22:38:22 cri
Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum Goma A Jihar AnambaraPublished 1 min ago on September 26, 2018 By Muhammad Baqeer Ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Anambara ta yi sanadiyyar mutuwar wata yarinya 'yar shekaru tara, mai suna Uzo Benedict a kauyen Amiyi dake karamar hukumar Ogbaru a yau Laraba 26 ga watan Satumba 2018. Al'amarin ya faru ne a yayin da yarinyar ta je dibar ruwa tare da yayarta 'yar shekaru 11 da haihuwa, yayar ta yi kokarin ceto ran kanwarta, amma haka ya jawo ta kusan yin asarar rayuwarta ita ma, cikin taimakon Allah makwota suka ceto ta. A cikin kwanakin nan ambaliyar ruwan ta kara Kamari, a inda wasu mutum biyu suka rasa ransu a jiya, a yau kuma Uzo ta rasa ranta, wannan ya kawo adadin wadanda suka rasa ransu ya kai mutum 10. hukumomi suna ta kokarin ankarar da mutane da yankin da ambaliyar ta fi shafa da su yi kokari barin wajen na dan wani lokaci, saboda a rage asarar rayuka da dukiya da ambaliyar take haifarwa. (Jaridar Leadership A Yau)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China