Sanarwar da shugabannin addinan suka fitar, ta yi tir da kisan kiyashin da sojoji da mayakan Amba Boys ke wa 'yan kamaru.
"Amba Boys" shi ne sunan da 'yan Kamaru ke kira 'yan awaren dake yunkurin neman kafa sabuwar kasa mai suna "Ambazonia".
Sanawar ta kuma ruwaito shugabannin addinan na yin tir da hare-haren da ake kai wa cibiyoyin ilimi da take hakkin yara na samun ilimi, suna masu sukar matakai marasa karfi da suka ce gwamnati ta dauka na shawo kan matsalar.
Shugabannin wadanda suka ce suna magana ne da murya daya kuma da yawun dukkan mabiya addinai, sun jadadda cewa, hawa teburin sulhu ne hanyar warware rikicin. (Fa'iza Mustapha)