in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Kamaru sun kashe 'yan aware 30 a yankin kasar dake amfani da Turanci
2018-09-19 13:25:06 cri

Rundunar sojin Kamaru, ta ce dakarunta sun kashe wasu da ake zargin 'yan aware ne a kauyen Njikwa dake arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankunan kasar biyu dake amfani da Turanci, wanda kuma ke fama da rikici.

Sanarwar ta ce da sanyin safiyar jiya Talata ne sojojin suka lalata sansanin 'yan ta'addar dake Njikwa, inda suka kashe 'yan aware sama da 30 tare da kwato makamai da dama. Gwamnatin Kamaru dai kan kira 'yan awaren ne da 'yan ta'adda.

A cewar rundunar sojin, biyu daga cikin dakarunta sun samu raunuka yayin samamen.

Rikici a yankuna 2 na arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar ya fara ne tun a bara, bayan da masu amfani da Turanci da suka fusata, suka ayyana 'yancin kan yankunan 2.

Kimanin kaso 20 na al'ummar Kamaru ne ke amfani da Turanci, yayin da ragowar 'yan kasar ke amfani da Faransanci. Kuma sun shafe gomman shekaru suna korafi game da wariyar da suke ikirarin ana nuna musu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China