A sakonsa na taya murna shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, zamantakewar al'umma tana begen samun zaman lafiya. Kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa cikin lumana, da kokarin shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa da ganin an martaba dokokin kasa da kasa a duniya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, taken ranar a wannan shekara shi ne "kokarin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da yin kokari tare wajen gina duniya mai cike da zaman lafiya da tsaro", wanda ya dace da tunanin da ya kai ga kafa ranar kiyaye zaman lafiya ta duniya da ma muradun kasashen duniya da al'ummominsu. (Zainab)