in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ai a Kamaru sun hana iyalai ficewa daga yankuna masu magana da yaren turanci
2018-09-16 15:25:56 cri
Hukumomi a yankin kudu maso yammaci, daya daga cikin wurare biyun da suke fama da tashin hankali masu magana da yaren Turancin Ingilishi a jamhuriyar Kamaru, a jiya Asabar sun hana wasu iyalai kaura zuwa yankin dake magana da yaren Faransanci a kasar.

Gwamna mai kula da shiyyar Bernard Okalia Bilia, ya shedawa 'yan jaridu cewa, ba wai suna hana mutanen yin bulaguro ba ne, sai dai sun hana masu kokarin kaura daga gidajensu ne wadanda ke kwasar kayayyaki don yin hijira, da suka hada har da kujeru da gadaje. Yace "idan sun tafi ina zasu je? Muna bukatar su zauna a gidajensu. Jami'an tsaro zasu tabbatar da ba su cikakkiyar kariyar".

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan da gungun mutane suka fara ficewa daga yankin mai fama da tashin hankali bayan barazanar da suke fuskanta daga mayakan 'yan arewa inda suka yi barazanar cewa za'a hana zirga zirgar ababen hawa gabanin fara zaben shugaban kasar a ranar 7 ga watan Oktoba.

Mayakan 'yan awaren sun yi barazanar dagula al'amurran zaben, sai dai Bilia ya ce, an dauki dukkan matakan da suka dace don gudanar da zaben cikin nasara.

Tun a watan Nuwambar bara ne, rikici ya kaure tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan arewa daga yankin arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar, yankuna biyu masu magana da yaren Ingilishi, yayin da kashi 80 bisa 100 na jama'ar kasar suna magana ne da yaren Faransanci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China