in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 40 sun nitse a tekun arewacin Morocco
2018-07-09 12:30:10 cri
Kimanin bakin haure 40 ne suka hallaka bayan da kwale kwalen da suke ciki ya nitse a tekun arewacin Morocco a jiya Lahadi, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

Bakin hauren da suka mutu sun fito ne daga kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika, kuma galibinsu mata ne, kamar yadda aka wallafa a shafin intanet na Moroccan Alyaoum24.com.

Rahotanni sun ce, an kai gawarwakin bakin hauren dakin adana gawarwaki na wani asibiti a birnin Larache, kuma ana cigaba da yin bincike domin gano masabbabin da ya haddasa hadarin.

Morocco ta kasance tamkar matattarar bakin haure daga kasashen Afrika wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Turai domin neman rayuwa mai inganci. Dubban 'yan cin rani ne ke kokarin tsallakawa Turai domin gujewa talauci da tashe tashen hankula dake ta'azzara a kasashensu, a duk shekara bakin hauren suna bi ta tekun Morocco ko ta hanyoyin kasa zuwa Turai, wadanda galibi suke amfani da rubabbun jiragen ruwa marasa inganci lamarin da ke jefa rayuwarsu cikin halin rashin tabbas.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China