A cikin sakon, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, sabbin fasahohin kimiyya suna samun ci gaba a fadin duniya, wadanda suka taimaka ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tare da kyautata hanyoyin inganta rayuwar dan Adam. Ya ce ya kamata a yi amfani da wannan dama da daidaita batutuwan da suka shafi harkokin kimiyya a fannonin dokoki, kiyaye tsaro, samar da aikin yi, da'a, tafiyar da harkokin gwamnati da sauransu, ya kamata kasashen duniya su zurfafa hadin gwiwa da tattauna kan wannan batun tare. Kasar Sin tana hada kai tare da ragowar kasashen duniya da more fasahohi da samun ci gaba da tabbatar da tsaro a wannan fanni tare da sauran kasashen duniya. (Zainab)