in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi da Putin, sun yi kira da a inganta abota tsakanin matasan kasashensu
2018-09-13 10:21:59 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun ziyarci cibiyar horar da yara ta All- Russian Children's Center da ake kira da "Ocean" a jiya Laraba, domin inganta abota tsakanin matasan kasashen biyu.

Shugabannin biyu sun kuma halarci bikin tunawa da cika shekaru 10 da cibiyar ta tsugunar da daruruwan yara Sinawa, da suka fito daga yankunan da mummunar girgizar kasa ta aukawa a shekarar 2008.

Da yake bayyana kasar Sin da Rasha a matsayin makwabta na kwarai kuma abokan hulda da tsaunuka da koguna suka hada su, wadanda ke tsayawa juna a lokacin bukata, Shugaba Xi ya ce al'ummar Sinawa da na Rasha, sun taimaki juna, kuma su kan taya juna farin ciki ko akasinsa, inda suke da tarihi mai taba zuciya.

Ya ce matasa su ne makomar kowacce kasa, kuma makomar abotar Sin da Rasha da ma ta duniya baki daya, yana mai kira ga matasan kasashen biyu, su inganta mu'amala da koyo daga juna, tare da kokarin dorawa kan abotar kasashen biyu.

A nasa jawabin, shugaba Putin ya ce Rasha da Sin sun kulla abotarsu ne bisa aminci da mutunta juna.

Ya ce abota tsakanin matasan kasashen zai kara karfafa tubalin dangantar dake tsakaninsu, kana ya na da muhimmanci ga makomar dangatakar kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China