in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aiktar kasuwancin Sin: Sin ta dauki matakin mayar da martani ga Amurka ne domin kiyaye tattalin arzikin duniya
2018-08-03 20:58:55 cri

Kwanan baya Amurka ta tsai da kudurin karin harajin kaso 25 bisa dari, kan kayayyakin da za ta shigo daga kasar Sin, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200 a don haka yau Jumma'a, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta kara sanya haraji iri hudu bisa dari kan kayayyakin Amurka wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 60. Kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne bisa doka kuma domin kiyaye tattalin arzikin duniya da muradun al'ummomi da kamfanonin kasashen duniya baki daya.

Jami'in ya kara da cewa, za a sanar da lokacin fara mayar da martanin bisa matakan da Amurka za ta dauka, kana idan ta ga tilas a dauki matakain, kasar Sin za ta dauki wasu sauran wajababbun matakai. Har kullum kasar Sin tana ganin cewa, ya dace a daidaita takaddamar cinikayya ta hanyar girmama juna da moriyar juna da kuma adalci, kalubale da yaudara za su lalata muradun bangarori daban daban ne kawai.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China