Bisa dokar cinikayyr waje ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin da dokokin da suka shafi sanya haraji kan kayayyakin shigi da fici ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin, majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince cewa, hukumar kula da harkar sanya haraji ta majalisar gudanarwar kasar ta tsai da kuduri cewa, za ta kara sanya harajin kaso 25 bisa dari ko kaso 20 bisa dari ko kaso 10 bisa dari ko kuma kaso 5 bisa dari kan kayayyakin kasar Amurka guda 5207 wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka kusan biliyan 60. Idan Amurka ta ci gaba da daukar matakan da ba su dace ba, ita ma kasar Sin za ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba.
A ranar 11 ga watan Yulin bana ne, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin da za ta shigo da su daga kasar Sin, wadanda dajararsu ta kai dalar Amurka biliyan 200, ya zuwa ranar 2 ga watan Agusta, wakilin cinikayyar Amurka ya bayar da sanarwar cewa, Amurka za ta kara sanya harajin da ya kai kaso 25 bisa dari. Matakan da Amurka ta dauka sun saba wa matsaya guda da bangarorin suka cimma, lamarin da ya kara tsananta takaddamar cinikayyar dake tsakaninsu, har suka sabawa ka'idojin hukumar WTO da tsarin cinikayya maras shinge, tare kuma da kawo illa ga muradun kasar Sin da al'ummar ta, kana za su hana ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.(Jamila)