in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana ra'ayi kan batun karin haraji kan kayayyakin Sin da Amurka za ta yi
2018-08-02 19:42:29 cri

Yau Alhamis kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin kwanakin nan, gwamnatin kasar Amurka ta dauki matakai guda biyu a lokaci guda, wato ta sanar da cewa, za ta kara sanya harajin kaso 25 bisa dari daga kaso 10 bisa dari kan kayayyakin da za ta shigo da su daga kasar Sin wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200 da kaso, a daya wajen kuma ta yi shelar cewa, tana son maido da shawarwari da kasar Sin kan batun cinikayya.

Kakakin ya nuna cewa, Amurka tana matsawa kasar Sin lamba, haka kuma tana yaudara kasar Sin, matakan da ta dauka ba su da amfani ko kadan, haka kuma za su sa ran kasashen da ke adawa da takaddamar cinikayya a fadin duniya ya baci.

Jami'in ma ya kara da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta zargi kasar Sin shi ne domin hana kasar Sin ta samu ci gaba cikin lumana, har kullum kasar Sin tana dauka cewa, ana iya yin amfani da damammaki iri iri, saboda tana cike da imani kan makomarta ta samun ci gaban tattalin arziki mai inganci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China