in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Ghana ya nuna gamsuwa kan hulda dake tsakanin Sin da Afrika da kuma Sin da Ghana
2018-08-15 21:12:10 cri

A yayin da yake zantawa da wakilin gidan radiyon kasar Sin a yau Laraba a ofishin jakadancin kasar Ghana dake birnin Beijing, jakadan kasar Ghana dake nan kasar Sin jakada Edward Boateng, ya bayyana dangantakar dake tsakanin Ghana da Sin a matsayin dangantaka mafi daraja kuma mai dadadden tarihi, a matsayinta na kasa ta biyu cikin kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da ta kulla dangantakar diflomasiyya da kasar Sin a shekarar 1960.

Jakadan na Ghana ya ce dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ta samo asali ne tun zamanin shugaban kasar Ghana na farko Osagyefo Kwame Nkrumah, a zamanin shugabancin jagoran jamhuriyar jama'ar kasar Sin na wancan lokaci Mao Zedong.Jakada Boateng ya ce, akwai kyakkyawan hadin gwiwa mai karfi ta fuskar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Game da batun taron dandalin hadin kan Sin da Afrika kuwa wanda kasar Sin za ta karbi bakuncinsa a watan Satumba mai zuwa, jakadan ya ce tun bayan kafa dandalin na FOCAC shekaru 18 da suka gabata, ya zuwa yanzu, an samu nasarori masu yawan gaske tsakanin bangarorin biyu, wanda a cewarsa hadin gwiwar ta baiwa kasashen Afrika damammaki masu yawa wajen samun ci gaba musamman ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa da yaki da fatara da kuma sana'o'in dogaro da kai da dai sauransu. Sannan ya yi amanna cewa kasar Ghana a shirye take ta cigaba da yin hadin gwiwa da Sin wajen cin moriya musamman a bangaren samar da hanyoyin layin dogo, tinunan mota, gine ginen gidaje da dai sauransu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China