Wasu alkaluma da gwamnatin jihar ta fitar, sun nuna cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai mutane 906, cikin watanni 2 da suka gabata.
A Juma'ar nan ne dai fadar gwamnatin ta Yobe, ta ayyana barkewar cholera a jihar, tana mai cewa cutar ta yadu cikin kananan hukumomin jihar 6.
Cutar amai da gudawa dai na yaduwa ne ta hanyar amfani da ruwa maras tsafta. (Saminu Alhassan)