in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar amai da gudawa ta hallaka mutane 97 a wasu jihohin Najeriya
2018-09-25 09:42:14 cri
Yawan mutanen da suka rasu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a jahohin Borno da Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya ya karu zuwa mutum 97.

Wasu alkaluma da ofishin tsare tsaren ba da agajin jin kai na MDD ko UNOCHA ya fitar ta cikin wani rahoto, sun nuna karuwar da aka samu game da yaduwar wannan cuta. Rahoton ya ce a jihohin Borno da Yobe, yawan wadanda suka kamu da cutar ta amai da gudawa mai haifar da gudawa mai tsanani sun kai 3,126.

Wasu kafafen watsa labarai na yankunan dake fama da wannan annoba sun bayyana cewa, mutane 36 sun rasu, bayan da suka kamu da cutar wadda ake dauka daga shan ruwa maras tsafta a jihar Borno.

Kawo yanzu dai cibiyar lura da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, ba ta yi wani karin haske game da yawan wadanda wannan cuta ta hallaka ba, sai dai a daya hannun, cibiyar ta ce yawan wadanda ke fama da cutattuka masu alaka da amai da gudawa sun kai mutum 16,353, tsakanin farkon wannan shekara ta bana ya zuwa yanzu.

Da yake tsokaci game da dalilan yaduwar wannan cuta, kwamishinan lafiya na jihar Yobe Muhammad Kawuwa, ya ce rashin isassun kayan kiwon lafiya, da ambaliyar ruwa sakamakon karuwar ruwan sama a sassan jihar, na daga cikin dalilan da suka haddasa yaduwar cutar.

Kwamishinan ya ce cikin watanni 2 da suka gabata, an sallami mutane sama da 795 daga asibiti, bayan da suka samu cikakkiyar jiyyar wannan cuta ta amai da gudawa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China