in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Tarayya Ta Najeriya Ta Ware Naira Biliyan Uku Don Dakile Ambaliyar Ruwa
2018-09-17 11:13:09 cri
Bisa labarin da muka samu daga shafin intanet na Leadership a Yau, an ce, hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA, ta karbi Naira biliyan uku domin amsa kira a duk lokacin da annobar ambaliyar ruwan da ake hasashe ta malalo, kasantuwar gargadin hakan da hukumar hasashen yanayi ta, NHISA, ta fitar.

Babban daraktan hukumar, Mustapha Maihaja, ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Abuja, sa'ilin da yake wata ganawa da masu ruwa da tsaki a hukumar ta NEMA, domin duba sakamakon rahotannin kwamitocin hukumar da suka zagaya duba irin barnar da ambaliyan ruwan ta haifar a Jihohin da abin ya shafa.

A cewar Maihaja, shugaba Buhari ya amince da baiwa hukumar Naira biliyan 3 a mataki na farko domin ta shirya tarban annobar da ake hasashenta. Ya ce, akwai abin damuwa a sakamakon rahotannin da kwamitocin suka zo da su, domin kuwa wasu jihohin da suka hada da, Neja, Kogi, Delta da Anambra, har ambaliyar ruwan ta fara shafan su.

"Mun taru ne a yau domin mu duba halin da ake ciki na gargadin hasashen annobar da ke tafe wacce aka bayyana ta a ranar 7 ga watan Satumba. Gargadin da aka yi ya sanya mun kafa wasu kwamitoci guda shida, wadanda suka kewaya jihohi 12." a cewar Maihaja. (Leadership a Yau)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China