in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a Kano ya haura 30
2018-09-18 09:55:59 cri
Gwamnatin jahar Kano dake arewacin Najeriya ta ce kawo yanzu adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar ambaliyar ruwa ya kai 31 a jahar.

A kalla gidaje dubu 10 ne ambaliyar ruwa ta lahanta ko kuma ta lalata su baki daya a kananan hukumomi 15 dake jahar, inda ambaliyar ruwan ta shafa.

Kano, wadda cibiyar ciniki da zuba jarice ta arewacin Najeriya, ta fara fuskantar ambaliyar ruwan ne tun a ranar 27 ga watan Augasta.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Kano Ali Bashir ya shedawa 'yan jaridu cewa, kimanin manoma dubu 35 daga yankuna 8 na jahar ne ambaliyar ruwan ta yiwa mummunar barna a jahar.

Mafi yawa daga cikin manoman ambaliyar ta share gonakinsu in ji Bashir.

Kungiyar manoman shinkafa ta jahar Kano ta ce mambobinta sun tafka hasarar sama da kadada dubu 5 na gonakin shinkafarsu.

A karshen watan Augasta hukumar hasashen ruwan sama ta kasar ta yi gargadin za'a iya samun ambaliyar ruwa a jahohi 7 na kasar, inda ta ce za'a iya samun tumbatsar wasu koguna.

Da ma dai hukumomin hasashen yanayin ruwan sama sun yi gargadin cewa kananan hukumomi 20 daga cikin kananan hukumomi 44 na jahar Kano za su iya fuskantar ibtila'in ambaliyar ruwan.

A kalla madatsun ruwa uku sun fara sakin ruwan bayan da adadin ruwa ya zarta matakin da madatsun ruwan zasu iya dauka a tekun Niger, inda ruwa ya fara malala zuwa wasu yankunan. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China