in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ba za ta tsayar da neman zaman lafiya ba, in ji Antonio Guterres
2018-09-22 16:44:03 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya ce, ana bukatar yanayin zaman lafiya don cimma jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030, don haka MDD ba za ta daina neman zaman lafiyar duniya ba domin tallafawa al'ummomin kasa da kasa.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 37 na ranar zaman lafiya ta kasa da kasa da ya gudana jiya a hadkwatar MDD dake birnin New York. Yayin bikin kada kararrawa ta zaman lafiya na gargajiya, Antonio Guterres ya bayyana cewa, adadin masu fama da talauci mai tsanani a duniya na raguwa, amma kuma ana fuskantar karin matsalolin rashin adalci, lamarin da kan tada hankulan jama'a, da haddasa yake-yake a tsakanin bangarori daban daban.

Ya ce, jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 na MDD, shi ne burin bil Adama na neman adalci, sabo da "in babu adalci, ba za a sami ci gaba ba, kuma in babu ci gaba, ba za a samu zaman lafiya ba".

Bugu da kari, ya ce, burin neman zaman lafiya ne dalilin da ya sa aka hadu a nan MDD, sai dai a halin yanzu, ana fuskantar kalubale wajen aiwatar da aikin, yana mai jadadda cewa MDD ba za ta daina fafutukar tabbatar da zaman lafiya ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China