in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Kamaru sun kashe 'yan aware 15 a yankin dake amfani da Turancin Ingilishi mai fama da rikici
2018-09-12 09:55:45 cri
Rundunar sojin Kamaru, ta ce dakarunta sun kashe 'yan aware 15, biyo bayan wani samame da suka kai sansaninsu dake garin Chomba na yankin arewa maso yammacin kasar, wato daya daga cikin yankunan kasar biyu dake amfani da turancin Inglishi, wadanda kuma ke fama da rikici.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce, an kama 'yan aware biyu, sannan an kwato bindigogi 13 nau'ika daban daban da kuma alburusai.

Wata majiya daga rundunar sojin ta shaidawa Xinhua cewa, babu sojan da ya rasa ransa yayin samamen, sai dai biyu daga cikinsu sun samu raunuka.

Tun watan Nuwamban bara, dakarun gwamnati ke arangama da 'yan aware masu dauke da makamai a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammci dake amfani da Turancin Ingilishi a kasar, mai mutane kaso 80 dake amfani da Faransanci.

'Yan awaren dai, sun ayyana 'yancin kan yankunan biyu, inda suke kiransu da "Ambazonia"

A cewar gwamnatin kasar, arangamar da ake tsakanin dakarun gwamnati da 'yan awaren ta yi sanadin mutuwar jami'an tsaro fiye da 100 da 'yan aware da ba a san adadinsu ba. amma wasu daga cikin jami'an sojin sun yi kiyasin cewa, sama da 'yan aware 200 aka kashe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China