Kwamitin wanda daukacin mambobinsa suka amince da kudurin mai lamba 2436, ya yi kira ga Sakatare Janar na MDD da ya tabbatar da shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na majalisar na da adalan shugabannin wadanda suka dace.
Sannan ya bukace shi, da ya sanya bayyanan ayyukan wanzar da zaman lafiya, wanda ya takaita matakan da aka dauka na inganta ayyukan shirye-shiryen da shawo kan kalubaken dake tattare da su, cikin rahoton da zai mikawa kwamitin.
Kwamitin ya bayyana damuwa game da zargin cin zarafi ta hanyar lalata da ake wa jami'an wanzar da zaman lafiya, tare da tabbatar da goyon bayansa ga manufar sakatare Janar na majalisar, ta rashin lamuntar kowanne irin nau'i na cin zarafi ta hanyar lalata.
Kwamitin ya kuma bukaci dukkan kasashe dake bada gudunmuwar 'yan sanda da dakaru da su tabbatar da jami'an sun kai mizanin MDD a fannin kwarewa da horo da kayayyakin aiki da kuma tabbatar da aiwatar da aikin da aka dora musu bisa nuna kwarewa da dabi'u na kwarai. (Fa'iza Mustapha)