in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta raba mutane dubu 30 da gidajensu a Najeriya
2018-09-16 15:41:37 cri
Hukumomi a jahar Edo dake shiyyar kudancin Najeriya sun sanar a jiya Asabar cewa, kimanin mutane dubu 30 ne suka rasa matsugunansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a wasu yankuna sama da 35 dake sassan jahar.

Shugaban karamar hukumar Etsako ta gabas, Aremiyau Momoh ya fadawa 'yan jaridu a Benin babban birnin jahar cewa, ibtila'in da ya faru ya fi karfin ikon da karamar hukumar ke da shi.

A nasa bangaren, John Akhigbe, shugaban karamar hukumar Etsako ta tsakiya, ya bukaci gwamnatin jahar da gwamnatin tarayya da su kai musu daukin gaggawa.

Jami'an biyu sun ce, tuni aka samar da wani sansanin tsugunar da mutane da ibti'ain ya shafa daga sassan kananan hukumon yankin.

Bugu da kari, kimanin gidaje 700 ciki har da wasu gonaki ne ambaliyar ruwa ta shafa bayan mamakon ruwan sama da aka sheka a yankunan jahar Rivers mai arzikin mai.

Martins Ejike, jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta kasar (NEMA), ya shedawa 'yan jaridu a Fatakol babban birnin jahar Rivers cewa, an fara fuskantar ambaliyar ruwan ne tun a watan Augasta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China