Guterres ya ce, halartar wadannan shugabanni gami da kusoshin gwamnatocin kasashe daban-daban, na shaida irin amincewar da kasashen duniya suke nunawa MDD. Guterres ya ce, zai yi amfani da wannan dama, don neman kasashe daban-daban, su yi sabon alkawari ga MDD, kasancewar ta dandalin tattauna hadin-gwiwar kasa da kasa da ba za'a iya rayuwa ba bu ita ba. Har wa yau, Guterres ya nuna damuwa, game da "yadda wasu bangarori daban-daban ke nuna kyama" ga ra'ayin halartar kasashe daban-daban a harkokin duniya.(Murtala Zhang)