in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta kudu sun lashi takobin hada gwiwa don samun zaman lafiya mai dorewa
2018-09-22 16:06:27 cri
Kasashen Sudan da Sudan ta kudu, sun jadadda kudurinsu na hada gwiwa don samun dawwammamiyar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen 2.

Kasashen 2 sun gudanar da wani taro a jiya Juma'a a fadar shugaban kasar Sudan dake Khartoum, karkashin jagorancin shugaban kasar Omar al-Bashir da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir.

Bayan ganawar, ministan harkokin wajen Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed, ya shaidawa manema labarai cewa, Shugaba Al-Bashir na Sudan, ya jadadda muhimmancin taron, yana mai nanata cewa, Sudan da Sudan ta kudu, kasashe ne 2 dake dauke da al'umma guda, kuma wannan tubali ne na shawo kan yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu da kuma tabbatar da cimmasa.

Ministan ya ce bangarorin biyu sun kuma bayyana aniyarsu ta aiki tare don samun zaman lafiya mai dorewa da inganta dangantaka a tsakaninsu.

A nasa bangaren, ministan labaran Sudan ta kudu Micheal Makuei, ya ce akwai alakar tarihi mai karfi tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa sun kasance al'umma guda a kasashe 2.

Ya kara da cewa, har yanzu suna neman Gwamnatin Sudan ta ci gaba da mara musu baya domin kawar da matsalolin da suke fuskanta na awaitar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China