in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fada ya barke a Sudan ta kudu bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
2018-09-16 15:19:54 cri
Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu na cewa,wani sabon fada ya barke a kasar, 'yan kwanaki bayan da bangaren gwamnati da kungiyoyin 'yan adawar kasar suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Habasha dake makwabata.

Sai dai kuma gwamnati da 'yan adawa na zargin juna da tayar da sabon fadan a sassan Kajo-Keji da Lainya.

Mataimakin mai magana da yawun sojojin babban kungiyar 'yan adawa kwatar 'yancin al'ummar Sudan (SPLA-I0) Lam Paul Gabriel, ya zargi dakarun gwamnati da fara kaiwa sansanoninsu hari a ranar Laraba, ranar da bangarorin da ba sa ga maciji da juna suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.

Ya ce, fadan ya ci gaba har zuwa ranar Jumma'ar da ta gabata, kuma an kashe a kalla sojojin gwamnati 8 yayin bata kashin na kwanaki uku, sai dai ba a tabbatar da wannan ikirarin ba.

Amma kuma mai magana da yawun sojojin gwamnati Lul Roai Koang ya karyata zargin 'yan adawar, yana mai cewa, farfaganda ce kawai. Yana mai cewa, 'yan tawayen ne suka fara tayar da fadan a yankunan kudanci da arewacin kasar, a kokarin da suke na kara kwace yankuna domin girke dakarunsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China