in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yabawa jami'ar aikin gona ta kasar Sin bisa tallafin ta ga raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa
2018-09-15 15:25:32 cri

Daraktan mai lura da ofishin raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a MDD Jorge Chediek, ya jinjinawa mahukuntan jami'ar ayyukan gona ta kasar Sin, bisa kafa wasu tsare tsaren hadin gwiwa guda biyu, na raya musaya a fannin noma da bunkasa ci gaba.

Mr. Jorge Chediek, ya bayyana hakan ne yayin wani taron masana, yana mai cewa kaddamar da shiri bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a fannin hadin gwiwar Sin da sauran kasashe masu tasowa, da shirin cibiyar Sin mai tallafawa hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin ayyukan noma, za su taimaka matuka wajen habaka bincike, da raya karkara, da musayar ilimi, da kirkire-kirkire tsakanin sassan duniya baki daya.

Ya ce noma sana'a ce daya tilo, wadda ke samar da kaso mai tsoka na sana'a ga al'ummun duniya. Bisa kididdiga, sana'ar na samarwa kaso 40 bisa dari na al'ummun duniya da damar dogaro da kai.

Daga nan sai ya sake jinjinawa Sin, bisa jagoranci da take yi a fannin raya aikin noma tsakanin kasashe masu tasowa, yana mai cewa ta taka rawar gani wajen raba sassan duniya da yunwa, ta hanyar kwarewarta, da taimako da take baiwa kasashe masu yawa.

Jami'in ya yi fatan cewa, karkashin wannan dama ta tattaunawa, za a samu damar yin koyi daga dabaru, da kwarewar kasar Sin a fannin noma, da ma koyon fasahohin raya ilimin noma, da ba da horo, da bunkasa binciken kimiyya, da ginawa, tare da karfafa ribar da ake samu daga cinikayyar hajojin noma ta hanyar amfani da na'urorin zamani.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China