in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya bukaci a dauki karin matakan yaki da rashawa
2018-09-11 10:26:10 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres a jiya Litinin ya bukaci dukkan mambobin kasashen duniya da su dauki karin matakan yaki da rashawa.

A halin yanzu matsalar rashawa ta zama ruwan dare a tsakanin dukkan kasashen duniya, masu arziki da matalautan kasashe, arewaci da kudanci, wadanda suka cigaba da masu tasowa, ya tabbatar da hakan ne ga kwamitin sulhu MDDr.

Ya ce wajibi ne mambobin kasashen duniya su tashi tsaye wajen yakar rashawa. Ya kara da cewa, abu ne mai matukar muhimmanci kasashe su kafa wani tsari na baiwa hukumomin yaki da rashawa kwarin gwiwa wajen hukunta dukkan laifukan dake da nasaba da rashawa.

Dandalin tattalin arziki na kasa da kasa yayi kiyasin ana tafka hasarar a kalla dalar Amurka trillion 2.6 ko kuma kashi 5 bisa 100 na GDP na kasashen duniya a sanadiyyar ayyukan rashawa.

A cewar bankin duniya, 'yan kasuwa da daidaikun mutane suna biyan dala biliyan 1 a duk shekara a matsayin cin hanci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China