in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar taron MDD tayi alkawarin karfafa gamayyar kasa da kasa don amfanawa kowa
2018-09-18 11:11:04 cri
Shugabar babban taron MDD karo 73 Maria Fernanda Espinosa Garces ta fada a jiya Litinin cewa, zata yi aiki tukuru domin kare matsayin gamayyar kasa da kasa domin tabbatar da ganin MDD tana amfanawa dukkan bil adama.

"Mun kudiri aniyar karfafa hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa," inji ta, jim kadan bayan da ta yi rantsuwar shugabancin taron MDD karo na 73 wato UNGA, ta kara da cewa "hanya daya tilo da za'a iya tunkarar kalubalolin duniya shine ta hanyar hadin gwiwa."

Espinosa Garces tace, tana matukar farin ciki da kasancewarta mace ta farko a yankin Latin Amurka da Caribbean wadda zata jagoranci babban taron MDDr.

Da take tsokaci game da abinda zata fi baiwa fifiko a lokacin aikinta a shekara mai zuwa, tace taken taron na UNGA karo na 73 shi ne "Shigar da kowa cikin shirin MDD. Kusato da MDD ga dukkan bil adama da gudanar da mu'amala tsakanin mutane da MDD, mayar da tsarin MDD a matsayin aikin da ya shafi bil adama."

A taron MDD na ranar 5 ga watan Yuni aka zabi Espinosa Garces, wadda ministar harkokin wajen kasar Ecuador ce, don ta kasance jagorar babban taron MDDr. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China