in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin Kamaru dake amfani da Turancin Ingilishi
2018-09-10 10:39:26 cri
Hukumomi a yanki arewa maso yammacin Kamaru, daya daga cikin yankuna biyu na kasar dake amfani da turancin Ingilishi, wanda kuma ke fama da rikici, sun ayyana dokar takaita zirga-zirga a baki dayan yankin.

Sanarwar da Gwamnan yankin Adolph Lele Lafrique ya fitar, ta ce daga jiya, ranar da aka ayyana dokar, babu zirga –zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a fadin yankin har sai baba-ta-gani.

Sanarwar ta ce a cikin wancan lokaci, dole ne shaguna da gidajen rawa su kasance rufe. Haka zalika tashoshin mota, sannan an dakatar da dukkan tafiye-tafiye da daddare.

An dauki wannan mataki ne bayan an kashe wani direban mota a wani hari da 'yan bindiga suka kai wa motocin bas-bas a yunkurinsu na balle yankin na arewa maso yammaci daga kasar.

Rikici na kara kamari a yankuna biyu na kudu masu yammaci da arewa masu yammacin kasar masu amfani da Turancin Ingilishi, gabanin zaben shugaban kasa na ranar 7 ga watan Oktoba.

'Yan aware masu son ballewa daga ragowar kasar mafiya rinjaye masu amfani da harshen Faransanci don son kafa Kasar "Ambazonia", sun lashi takobin hana gudanar zabe a yankunan kasar 2 masu amfani da Turancin Ingilishi.

A cewar gwamnatin kasar, rikicin ya yi sanadin mutuwar sama da jami'an tsaro 100 da 'yan tawayen da ba a san yawansu ba. sai dai sojojin kasar sun yi kiyasin an kashe sama da yan tawaye 200. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China