Jiya da yamma ne aka bude babban taron MDD karo na 73 a cibiyar MDD dake birnin New York. Taken taron na wannan karo shi ne "Yadda MDD za ta yi tasiri ga daukacin al'ummar duniya, raya duniya mai zaman lafiya da adalci mai dorewa ta hanyar inganta tafiyar da harkokin duniya da daukar nauyi yadda ya kamata". (Zainab)