in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi na'am da sakamakon taron kasashen Koriya 2
2018-09-20 15:31:25 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi na'am da sakamakon taro karo na 3 da aka yi a bana, tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da ta Kudu.

Wata Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ce Sakatare Janar din ya yaba da jajajircewa da salon diflomasiyyar da suka kai ga cimma muhimmiyar yarjejeniya a Pyongyang.

Sanarwar ta ce kudurin da aka dauka karkashin yarjejeniyar ya hada da matakan kwance damarar soji da kuma kudurin koriya ta arewa na lalata wajen da take gwajin makaman nukiliya a gaban kwararru daga kasashen dake da ruwa da tsaki game da batun, ta na mai cewa lokaci ya yi da ya kamata a dauki kwakkwaran mataki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China