Darekta kana wakiliyar ofishin hukumar mai kula da nahiyar Afirka, Juliette Biao Koundenoukpo ita ce ta bayyana hakan yayin bude taron dandalin manyan kungiyoyi da masu ruwa da tsaki na Afirka na kwanaki biyu da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Tana mai cewa kasashen nahiyar za su iya amfani da hanyoyi da matakan su na diflomasiya wajen canja ajandar nahiyar game da muhalli.
Ta ce kungiyoyin gama kai za su taimaka wajen inganta matakan kirkire-kirkire na kasashen nahiyar game da tunkarar kalubalen muhalli da nahiyar take fuskanta.
Jami'ar ta ce, akwai bukatar kasashen na hanzarta canjawa daga tsarin da aka saba gudanarwa a baya zuwa hanyoyi da matakan da suka dace domin magance batutuwa kamar karuwar tsadar kudaden makamashi da batun talauci da lalacewar muhalli, da gurbatar iska da rashin daidaiton tsakanin jama'a.
Ta ce, kasashen nahiyar na da karfi da ilimin kirkiro matakan magance kalubalen muhalli da suke fuskanta. (Ibrahim)