in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren jam'iyya mai mulki a Kenya ya ce Sin ba za ta yi mulkin mallaka a Afirka ba
2018-09-21 11:00:33 cri
A kwanakin baya ne, aka yi bikin kafa babbar kungiyar 'yan kasuwan lardin Sichuan da birnin Chongqing na kasar Sin dake kasar Kenya, inda babban sakataren jam'iyyar Jubilee mai mulkin Kenya, Raphael Tuju, ya karyata rahotannin dake cewa kasar Sin na tafiyar da sabon salon mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Tuju ya ce, kasar Sin ba ta taba mallakar wani yanki a nahiyar Afirka ba, balle ma ta yi mulkin mallaka a Kenya. Har wa yau, baya ga Kenya, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a sauran kasashen Afirka ba.

Tuju ya ce, duk da cewa akwai bambance-bambance tsakanin al'adu da addinai na Sin da Kenya, ana samun kamanceceniya da dama a wajen halayen dan Adam a tsakanin al'ummomin kasashen biyu, al'amarin da ya sa jama'ar kasashen ke iya kulla zumunta da juna.

Tuju ya ce, kasar Sin ta samu dimbin nasarori ne a cikin shekaru arba'in kawai, yana mai cewa babu wata kasa da ta taba samun irin wadannan manyan nasarori a cikin kankanin lokaci.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China