in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren jam'iyya mai mulkin kasar Kenya ya bayyana ra'ayinsa kan makomar hadin-gwiwar Sin da Afirka
2018-09-18 11:21:07 cri
A kwanakin baya ne ba da jimawa ba, aka rufe taron koli na dandalin tattuana hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Beijing na kasar Sin. A halin yanzu shugabanni gami da manyan jami'an gwamnatocin kasashen Afirka daban-daban na nan na kokarin tabbatar da sakamakon da aka samu a wajen taron kolin, gami da kara fadada hadin-gwiwarsu da kasar Sin.

Jiya Litinin, babban sakatare na jam'iyyar Jubilee mai mulkin kasar Kenya, Raphael Tuju, ya bayyana cewa, an cimma manyan nasarori da dama a wajen taron kolin FOCAC a wannan karo, kuma akwai makoma mai haske game da hadin-gwiwar Sin da Afirka. Ya ce, ya kamata kasashen Sin da Kenya su yi kokarin neman ci gaba tare, yana mai jadadda cewa, taron kolin na da muhimmancin gaske ga dangantakar Sin da Afirka da ma Sin da Kenya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China