Aikin layin dogon na Nairobi-Naivasha SGR mai nisan kilomita 120, shi ne kashin farko na bangarori uku wanda zai kasance kashi na biyu na aikin gina layin dogon wanda zai kare a garin Malaba dake yankin iyakar kasashen Kenya da Uganda.
Aikin na Nairobi-Naivasha SGR, zai kawo babbar moriya wajen saukaka harkokin sufuri na zirga zirgar fasinjoji da kuma dakon kayayyaki wanda zai taimaka matuka wajen bunkasa harkokin cinikayya da bunkasuwar masana'antu.
Kafa yankin tattalin arziki na musamman wato (SEZ) a yankin Mai Mahiu/Suswa zai kasance wani muhimmin ginshikin tabbatar da wannan aikin gina titin jirgin kasan na zamani. (Ahmad Fagam)