in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta karbi bakuncin taron farfado da gonakin da suka lalace a Afrika
2018-08-02 10:25:11 cri
Sama da wakilan hukumomi da masana kimiyya da masu rajin bunkasa noma 800 ne za su hallara a Nairobi cikin wannan wata da muke ciki domin lalibo hanyoyin fasahar farfado da gonakin noma da suka durkushe a nahiyar Afrika, kamar yadda mashirya taron suka sanar a ranar Laraba.

Taron dandalin na wuni biyu wanda cibiyar nazarin gandun daji ta (CIFOR) ta shirya, tare da hadin gwiwar hukumar kare muhalli ta MDD da bankin duniya, inda ake son mayar da hankali wajen dakile hanyoyin dake haifar da lalacewar gonakin noma da dazuka wanda halayyar bil adam da kuma sauyin yanayi ke yin barazana ga gonakin da kuma dazuka.

Darakta janar na cibiyar CIFOR Robert Nasi ya ce, tilas ne a farfado da filayen Afrika domin kiyaye albarkatun kasa dake jibge a nahiyar don ganin an samu damar cimma muradun yawan al'ummar dake karuwa a nahiyar nan da wasu lokuta masu zuwa.

An yi kiyasin ana lalata gonaki kimanin kadada miliyan 50 a duk shekara a fadin kasashen dake hamadar saharar Afrika sakamakon sakaci na rashin daukar matakan da suka dace daga bangaren hukumomi, da yawan karuwar jama'a, da sauyin yanayi da kuma kaura zuwa birane.

Nasi ya ce, za'a gudanar da taron dandalin ne daga ranar 29 zuwa 30 ga wannan wata na Augasta inda za'a tattauna game da kwararan matakan da za'a dauka wajen gaggauta farfado da gonakin don bunkasa samar da abinci, da rage talauci da kaucewa lalata albarkatun kasa.

Mashirya taron sun ce bayanan ilmi da musayar kwarewar da za'a tattaro a lokacin taron, za'a yi amfani da su wajen daukar matakan farfado da gonaki da kuma dazuka wadanda suka tasamma durkushewa a 'yan shekarun nan a Afrika.

Erik Solheim, babban daraktan hukumar kare muhalli ta MDD ya ce, akwai bukatar a gaggauta maido da gonaki da dazukan Afrika domin baiwa nahiyar damar cimma muradun da ake da su na samar da abinci don ciyar da dubun al'ummar kasashen dake kara yawa.

Cibiyar nazarin albarkatun kasa ta duniya ta yi kiyasin cewa, biyu bisa uku na yawan filayen dake Afrika an lalata su yayin da kusan kadada miliyan 2.8 na dazukan nahiyar an share su sun koma gonaki ko kuma gidajen zaman jama'a. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China