Shugban dandalin Yang Tao, ya ce kamfanin da aka kafa a shekarar 2014, ya fara aiki a kasashen Uganda da Nijeriya a bara.
Yang Tao ya shaidawa wani ayarin Sinawa masu zuba jari dake neman damarmaki a bangaren cinikayya ta intanet na kasar Kenya cewa, suna shirin shiga dukkan kasashen Afrika ya zuwa karshen 2022, domin biyan bukatar cinikayya ta intanet da ke karuwa.
Ya kara da cewa, an fara kafa dandalin ne a Kenya la'akari da yadda kasar ta fi kowacce kyan yanayin kasuwanci a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)