Jami'ar wadda ta shaidawa 'yan jaridu hakan a birnin Nairobin kasar Kenya, ta ce yanzu haka kasar dake kudancin Afirka ba ta haramta cinikin hauren giwa a cikin gida ba, kuma hakan na iya kassara kokarin da ake na kare giwayen dake nahiyar ta Afirka. Mwakima ta ce, ya zuwa yanzu, sama da kasashen Afirka 30 da Allah ya hore musu albarkatun giwaye dake tsakiya da yammacin Afirka na goyon bayan matakan da Kenya ke dauka na kare rayukan giwayen.
Bayanai na nuna cewa, an sanya adadin giwayen da kasashen Botswana da Namibia da Afirka ta kudu suke da su a cikin muhimmiyar takarda ta biyu na taron cinikayyar kasa da kasa game da dabbobin dake daf da karewa a muhallin halittu (CITES), wannan na nufin cewa, an ba su damar yin cinikin hauren giwa, a dai-dai gabar da aka sanya giwayen dake ragowar kasashen Afirka cikin muhimmiyar takarda ta farko wadda ta haramta cinikin hauren giwa.
Jami'ar ta kuma bayyana cewa, galibin kasashen Afirka, sun amince a sanya dukkan giwayen cikin muhimmiyar takarda ta farko a yayin taron CITES da zai gudana a watan Mayun shekarar 2019 a Sri Lanka. (Ibrahim)