in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Japan sun sha alwashin karfafa dangantakar kasashen su
2018-09-12 13:58:14 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan kasar Japan Shinzo Abe, sun yi wata ganawa a Larabar nan, inda suka jaddada aniyar su ta karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen su, suna masu alkawarin daukar nauyin yayata burin wanzar da zaman lafiya da lumana, a matakan yankuna da ma na kasa da kasa.

Kaza lika sun sha alwashin daukar karin matakai na samar da ci gaba, da walwala ga al'ummun duniya.

Shugabannin biyu sun gana ne a birnin Vladivostok na kasar Rasha, a gefen taron dandalin tattauna batun tattalin arziki, na yankin gabashin duniya karo na 4, wanda ke gudana yanzu haka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China