Kwamandan ya ce, 'yan tawaye na amfani da wadannan makamai ne wajen kaiwa jami'an tsaro hari. Ya ce, yanzu haka sojojin sun yi nasarar kwace kimanin makamai 837 baya ga wuraren kera makamai da dama na mayakan da sojojin suka tarwatsa. An kuma kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar da mayakan ke amfani da su wajen shigo da makamai ta barauniyar hanya.
Da yake karin haske ta kafar talabijin din kasar, Janar Ndong ya ce, karuwar bazuwar haramtattun makamai a yankin, wata babbar barazana ce ga harkokin tsaro.
Alkaluman hukuma na nuna cewa, an samu karuwar bazuwar haramtattun makamai a kasar ta Kamaru, tun lokacin da aka fara samun tashin hankali a yankin da ake magana da turancin Ingilishi na kasar.
Koda a wata a Afrilun wannan shekara, sai da gwamnati ta haramta saye da sayar da makamai a yankuna shida na kasar, biyo bayan karuwar mallakar haramtattun makamai a bangaren fararen hula daga 340,000 a shekarar 2007 zuwa 510,000 a shekarar 2017. (Ibrahim)