in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kamaru da UNICEF sun yi tir da harin da aka kaiwa 'yan makaranta a yankin arewa maso gabashin kasa
2018-09-07 10:01:48 cri
Shugaban Kamaru Paul Biya, ya yi tir da harin da aka kai kan yara 'yan makaranta a arewa maso gabashin kasar, daya daga cikin yankuna 2 na kasar dake amfani da turancin Ingilishi.

Ministan yada labarai kuma kakakin shugaban kasar Issa Tchiroma, ya ce Shugaban kasar ya umurci gwamnati ta dauki matakan da suka dace na tabbatar da harkokin makarantu sun gudana lami lafiya a kasar.

Shi ma asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ta bakin wakilinsa a Kamaru, Jacques Boyer, ya yi tir da harin da ya kai ga sace yara 'yan makaranta, yana mai cewa dole ne yara a yankunan da sauran yankunan kasar, su rika zuwa makaranta ba tare da fargaba ba, yana mai kira da a tabbatar da kare 'yancin dukkan yara.

Tun da aka fara sabon zangon karatu a ranar 3 ga watan Satumba, aka fara kai hare-hare kan makarantu da shugabanninsu da dalibai da malamai a yankunan biyu.

A ranar Talata da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wata makaranta a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka sace dalibai 6 da shugaban makarantar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China