Liu ya bayyana haka ne a yayin taron harkokin kawar da talauci da samun ci gaba na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka na shekarar 2018, wanda aka shirya yau a nan birnin Beijing. Ya kara da cewa, kawar da talauci da tabbatar da samun dauwamammen ci gaba sun kasance buri da aikin bai daya na jama'ar Sin da na kasashen Afirka. Kokarin yin cudanya da hada kai a fannin kawar da talauci ita ce hanya mai muhimmanci ta tabbatar da samun ci gaba tare, da gina al'umma mai kyakyyawar makoma ga bangarorin biyu. Don haka, ya kamata su karfafa hadin kai a wadannan fannoni guda hudu, kamar kara yin musanyar ra'ayoyi, da nazari tare, da horar da kwararrun matasa, da kuma gudanar da shirye-shiryen da za su zama misali a fannin kawar da talauci. (Bilkisu)