in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawa tsakanin al'ummomin Sin da Afirka karo na 5
2018-07-23 20:14:07 cri

A yau Litinin ne aka bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin al'ummomin Sin da kasashen Afirka karo na 5 a birnin Chengdu na kasar Sin. Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya halarci bikin bude taron, tare kuma da ba da jawabi.

A cikin jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aiko da wasika, don taya murnar shirya taron, wannan ya nuna cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar, sun dora muhimmanci sosai, kan mu'ammala da hadin kai a tsakanin al'ummomin bangarorin biyu. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna sahihancin ra'ayi, da nufin ciyar da dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka gaba.

Baya ga haka, Wang ya kuma gana da shugaban jam'iyyar Seychelles People's, kuma mataimakin shugaban kasar ta Seychelles Vincent Meriton, da kuma firaministan kasar Kongo Brazaville Clément Mouamba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China