in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa tsakanin ICBC da Bankin Standard ya bunkasa cinikayya da zuba jari
2018-07-24 13:22:52 cri

Shugaban Bankin Standard dake birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu Sim Tshabalala ya ce hadin gwiwar manya tsare-tsare na tsawon sama da shekaru goma tsakanin bankin na Standard da takwaransa na ICBC na kasar Sin, ta bunkasa alakar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Shugaban wanda ya bayyana hakan jiya Litinin, ya ce alakar sassan biyu ta kuma kai ga zuba jarin biliyoyin daloli a fannin gina ababan more rayuwar jama'a a kasashen Afirka ta dama, da taimakawa 'yan kasuwar nahiyar, da ma ingantuwar zirga-zirgar hajoji.

Jami'in ya ce, alakar ta kuma taimaka wajen saukaka harkokin cinikayya da zuba jari a nahiyar Afirka, matakin da zai taimaka matuka ga raya nahiyar.

Jami'in na wadannan kalamai ne yayin bikin cika shekaru 10 da kulla alaka tsakanin manyan hukumomin kudin biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China