Sheriff Ghali Ibrahim, shehun malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa a Jami'ar Abuja dake Nijeriya ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da kamfanin dillacin labarai na Xinhua.
Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce kamar kowacce nahiya a duniya, Afrika na samun kwarin gwiwa daga ci gaban kasar Sin, ya na mai cewa kasar Sin na zaburar da Afrika. Ya ce kayakin more rayuwa da Sin ta gina a Afrika sun samar da ci gaban da zai kai Afrika ga wani sabon mataki.
Cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu dimbin ci gaba ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa bisa aiwatar da manufarta ta yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare.
Da hadin gwiwarta da kasar Sin, Afrika na fatan ita ma za ta samu ci gaba wata rana. Domin ta hanyar hadin gwiwarta da kasar Sin, nahiyar Afrika ta bude kofarta, musammam ta dandalin tattauna hadin gwiwar bangarorin biyu. (Fa'iza Mustapha)