in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi maraba da shawarar kwamitin sulhu na MDD game da fitar da man fetur ta haramtacciyar hanya
2018-09-19 11:02:33 cri

Kamfanin mai mallakar gwamnatin Libya, ya yi maraba da shawarwarin da kwamitin kwararru na kwamitin sulhu na MDD ya gabatar game da fitar da mai daga kasar ba bisa ka'ida ba.

Sanarwar da kamfanin ya fitar, ta ce cikin rahotonsa na baya-bayan nan, kwamitin kwararrun, ya bada shawarwarin shawo kan yadda kamfanin man dake da mazauni a gabashin kasar, ke ci gaba da yunkurin fitar da mai ta haramtacciyar hanya ba tare da samun nasara ba, da sauran wasu muggan ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai wanda ke kaiwa ga karkatar da arziki kasar da tabarbarewa hukumomin da ababen more rayuwa.

Libya na fama da rarrabuwar kawuna sanadiyyar siyasa, tsakanin hukumomin gabashi da yammacin kasar, wadanda ke fafutukar neman halacci, ciki kuwa har da kamfanin mai na yankunan.

Makonni biyu da suka gabata ne kwaitin ya mika rahotonsa na karshe da ya zargi kamfanin mai dake da mazauni a gabashin kasar da yunkurin fitar da danyen man fetur ta haramtacciyar hanya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China