A wata sanarwar hadin gwiwa ta shugabannin kabilun kimanin 1,800 na Libya sun ce, kabilun kasar sun shiga cikin damuwa game da halin da ake ciki, bayan tashin hankalin da ya barke, wanda ya jefa 'yayansu cikin matsanancin hali, da rasa hakkokinsu, da kwace musu duk wata damar siyasa da suke da ita sakamakon yadda mayakan suka kwace dukkan madafun iko da duk wani ikon fada a ji a kasar.
Sanarwar ta kuma bukaci mayakan a babban birnin kasar Tripoli da su mika makamansu kuma a rusa dukkan hukumomin gudanarwar kungiyoyin mayakan bayan an raba su da makamansu.
A 'yan kwanakin da suka gabata ana fuskantar karuwar tashin hankali tsakanin dakarun gwamnati da mayakan runduna ta 7 daga Tarhuna, lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan mutane 78 da kuma jikkata wasu 210. (Ahmad Fagam)