A ranar Talata, kwamitin sulhun MDDr ya yanke shawarar kakabawa Jathran takunkumin hana tafiye tafiye, da daskaras da kadarori. Kafin hakan, babban mai shari'ar kasar ta Libiya, ya fitar da sammacen cafke jagoran na 'yan tawaye bayan aukuwar wani harin na daban, a sansanin dake kunshe da ma'adanar mai mafi girma a kasar, wadda ke da nisan kilomita 500 daga gabashin birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
Harin na baya, wanda kungiyar Jathran ta kaddamar ya auku ne a watan Yunin da ya shude, lokacin da dakarun ta suka kai farmaki a yankin, suka kuma kwace kusan rabin sa, kafin daga bisani dakarun gwamnatin kasar tsagin gabashi su fatattake su, a wata arangama da ta yi sanadiyyar kisan sojoji 34. (Saminu Alhassan)