in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin kasar Libya ta zargi IS da kaddamar da hari kan kamfanin mai dake Tripoli
2018-09-11 10:43:37 cri
Kakakin rundunar sojojin gwamnatin kasar Libya mai helkwata a gabashin kasar Ahmad al-Mismari, ya zargi kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS, da kaddamar da hari kan kamfanin man fetur na kasa dake birnin Tripoli, fadar mulkin kasar.

Ahmad al-Mismari ya tabbatar da hakan, yayin zantawa da manema labarai a birnin Benghazi. Ya ce suna da shaidu da cikakkun bayanai, dake nuna cewa mayakan IS da hadin gwiwar al-Qaeda ne suka kaddamar da harin na ranar Litinin, da ma wasu hare hare na baya da aka kaiwa helkwatar babbar hukumar zaben kasar.

Jami'in ya kara da cewa, ga alama wadannan hare hare somin tabi ne kawai, don haka ya wajaba ga daukacin hukumomin tsaro dake Tripoli, su yi namijin kokari wajen daukar matakan dakile karuwar su.

Da sanyin safiyar ranar Litinin ne dai wasu mahara dauke da muggan makamai, suka farwa helkwatar kamfanin man kasar, inda nan take suka hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu mutanen goma. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China