UNSMIL ya fada cikin wata sanarwa cewa, yayi maraba da zaben majalisun yankunan Bani Walid da Derj. Kwamitin shirya zabukan majalisun kananan hukumomin ya cancanci yabo saboda shirya zaben, inji sanarwar.
Shirin raya cigaba na MDD (UNDP) a Libya, ya sanar a ranar Asabar cewa, Jamus zata samar da euro miliyan 2 kwatankwacin dala miliyan 2.33 ga kasar Libya domin shirya zabuka tsakanin shekarun 2018 zuwa 2020, yayin da hukumar shirya zabukan majalisun yankunan (CCMCE) ta sanar da fara zabukan a biranen Bani Walid da Derj dake kudu maso yammacin Libya.