in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in kula da harkokin jin kai na MDD ya yi kira da a kare fararen hula a yankin tsaro na Idlib
2018-09-19 10:52:33 cri
Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Mark Lowcock ya yi kira da a kare rayukan fararen hula a yankin tsaron da ake son kafawa a lardin Idlin na kasar Syria.

Jami'in na MDD ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDD, yana mai cewa, idan har ya zama dole fararen hula daga ciki ko wajen yankin tsaron da ake fatan kafawa za su kwashe ya nasu ya nasu, wajibi ne a bar su su nemi mafaka a wani waje na daban.

Lowcock yana magana ne game da yarjejeniyar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin suka cimma da takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdowan a jiya Litinin na neman kafa yankin tsaro da babu sojoji a cikinsa a yankin Idlib.

Ya ce, ko da za a raba mutane da muhallansu a yankin tsaron, wajibi ne a dauki dukkan matakan da suka dace na samarwa fararen hula da shirin zai shafa matsuguni da, muhalli mai tsafta da kiwon lafiya da tsaro da abinci mai gina jiki, kana ba za a raba 'yan uwa da iyalansu ba.

Jami'in ya kara da cewa, yana da muhimmanci a tantance tsakanin fararen hula da mayaka kamar yadda dokokin jin kai na kasa da kasa suka tanada, a kuma tsara matakan gudanar da ayyuka, da tabbatar da cewa ana kare martaba dan-Adam da daukar nauyin wadanda aka riga aka tantance.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China