in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta ba Syria gudunmuwar motocin daukar mara lafiya da asibitocin tafi da gidanka
2018-08-17 11:14:02 cri
Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin, ta bada gudunmuwar asibitocin tafi da gidanka da motocin daukar mara lafiya, ga takwararta ta kasar Syria, wato Syria's Arab Red Crescent (SARC).

An mika gudumuwar da ta hada da motocin bus 2, da za a iya mayar da su asibitin tafi da gidanka da motocin daukar mara lafiya 2, yayin wani biki da aka yi a Damascus babban birnin Syria.

Gudunmuwar na da nufin taimakawa al'ummar Syria dake zaune a yankunan dake da wuyar isa ko kuma mutanen dake bukatar agajin gaggawa.

Wang Qinglei, wakilin kamfanin kera motoci na Beiqi Foton, da ya tallafawa gudunmuwar karkashin RedCross ta kasar Sin, ya shaidawa Xinhua cewa, asibitocin na tafi da gidanka na dauke da injunan daukar hoto na X-ray da Scan da na farfado da bugun zuciya da duba mara lafiya daga nesa tare da tsarin bada kulawa.

Ya ce wadannan injinan ne suka mayar da motocin asibitin tafi da gidanka, wanda zai iya bada kiwon lafiya cikin gaggawa da sakamakon gwaje-gwaje da kuma kananan tiyata.

Motocin na amfani ne da injin samar da lantarki, wanda zai ba su damar yin aiki a yankunan da babu lantarki.

Wang ya ce gudunmuwar da kamfaninsu ya bayar ta kai yuan miliyan 6 kwatankwacin dala 900,000, kuma ta na daya daga cikin matakin farko na jimilar agajin jin kai da Kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta shirya ba Syria, da kudinta ya kai yuan miliyan 8. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China